Isa ga babban shafi
Rayuwata

Talauci ya hana mata masu juna biyu koshi a Najeriya

Wallafawa ranar:

Shirin Rayuwata na wannan rana ya yi nazari ne kan rahoton Hukumar Kula Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya da ke cewa, adadin mata masu shayarwa da ke fama da tamowa ya karu da kashi 25 a duniya, inda a Najeriya wasu matan suka bayyana wa RFI Hausa irin yadda talauci ya hana su koshi duk kuwa da juna biyun da suke dauke da shi.

Ana son mace mai juna biyu ta rika samun isassen abinci domin dan tayin da ke cikinta..
Ana son mace mai juna biyu ta rika samun isassen abinci domin dan tayin da ke cikinta.. © Pixabay
Talla

Sama da mata da 'yan mata biliyan guda ke fama da karancin abinci mai gina jiki da karancin jini a sassan duniya kamar yadda rahoton ya yi bayani.

Rahoton ya ce, wannan matsalar ta fi kamari ne a kasashen duniya masu tasowa.

Shirin ya tattaunawa da kwararru har ma da wasu matan da ke fama da irin wannan matsalar ta rashin cin abinci mai gina jiki bayan haihuwa.

Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Zainab Ibrahim

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.