Kasuwancin tufafin kawa daga bangaren matasa a Afirka na kara fadada, inda matasan nahiyar ke tafiyar da ita, daidai da zamani.
Kayayyakin sawa daga Afirka na kara samun karbuwa a kasashen duniya, kuma matasan 'yan kasuwa na cin gajiyar wannan tsari ta hanyar sarrafa tufafi na musamman da kuma ba da gudummawa ga sauyin tattalin arzikin nahiyar.
Hakan ya samar da damammaki ga matasa masu sana'ar dinki.
Kuma kan wannan batu ne, Zainab Ibrahim ta leka Jamhuriyar Nijar domin duba irin basirar da suke zubawa a wannan fanni.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu