Shirin Rayuwata na wannan rana ya gayyato wasu mata da suka bayyana masa mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki sakamakon rashin barci, inda daya daga cikinsu ke cewa, yadda take ganin rana, to haka take ganin dare, yayin da iyayenta suka garzaya da ita asibiti don nema mata magani.
Kwararrun likitoci sun ce, ana bukatar mutun baligi ya rika samun barcin akalla sa'o'i bakwai zuwa takwas a kowacce rana domin samun cikakkiyar lafiya da kuzarin gudanar da al'amuran rayuwarsa.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Zainab Ibrahim
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu