Shirin Rayuwata na wannan rana ya yi nazari ne kan irin kalubalen da matan aure da mata masu juna biyu ke fuskanta a makarantun boko.
Talla
Shirin ya tattauna da wasu mata a Najeriya da suka shaida masa irin ukubar da suke sha a kokarinsu na hada karatu da daukar ciki ko kuma renon jariri.
Tuni kungiyoyin kare hakkin bil'adama suka bukaci samar da yanayi mai kyau domin samar da sauki ga ire-iren wadannan mata masu kokarin inganta rayuwarsu ta hanyar zurfafa ilimi.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Zainab Ibrahim.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu