Isa ga babban shafi
Rayuwata

Ko me ke janyo rashin auren wuri ga wasu matan?

Wallafawa ranar:

Masu iya magana kan ce mutunci kowacce ‘ya mace dakin mijinta, dalilin da ya sa iyaye ke yin duk mai yiwuwa wajen tarbiyantar da ‘ya’yan su mata su kuma rike su hannu bibiyu har ranar da zasu aurar da su.

Wasu mata dake aikin gonan lambu a kasar India
Wasu mata dake aikin gonan lambu a kasar India ASSOCIATED PRESS - SUDIPTO DAS
Talla

Toh amma kowa da yadda ya karbo tsarin rayuwarsa daga Ubangiji, domin kamar yadda wasu matan ke samun mazan aure cikin sauki, haka wasu ke shafe dogon lokaci kafin su shiga gidan aure, haka ma kamar yadda was uke dacen mazan auren, wasu matan kuwa akasin haka kan same su.

A yau shirin Rayuwata ya duba yadda da yawa daga cikin 'yan mata ke kokawa a kan rashin tayin aure, na gaskiya kuma ba na masu yaudara ba.

A halin da ake ciki a yanzu haka, yawancin ‘yan matan dake wannan koke sunce ko a gidan biki samari basu cika kula mata ba kamar yadda aka saba gani a da, duk kuwa da yadda su ke sheka Ado da kwalliya na daukar hankali

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakaken shirin tare da Zainab Ibrahim.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.