Libya
Libya za ta kara yawan mai da take fitarwa
Sakatare Janar na Kungiyar kasashen dake hako man fetur, OPEC, Adbullah El-Badri yace yanzu haka kasar Libya na fitar da gangan man fetur sama da million daya.Ya fadi cewa nan da nan da tsakiyar shekara mai kamawa ko shakka babu zata kai yawan abinda take samarwa kafin fara yakin da ya afkamata.Ya fadawa taron manema labarai bayan taron kungiyar Ministocin Man a birini Vienna na kasar Austria, cewa kasar ta Libya na bukatar wasu ganga dubu dari shida duk rana kafin ta kai adadin da take hakowa kafin yakin kawar da marigayi Moammar Gaddafi.
Wallafawa ranar: