Isa ga babban shafi
Bankin duniya

Bankin Duniya ya rage hasashen samun ci gaban tattalin arzikin duniya

Bankin Duniya ya rage hasashen sa na samun ci gaban tattalin arzikin duniya na bana, inda yayi gargadin cewar basusukan kasashen da suka fi arziki a duniya, na iya haifar da matsalar tattalin arzikin da zai zarce na shekarar 2008.Rahotan hasashen da bankin kan bayar sau biyu a kowacce shekara, ya nuna koma bayan tattalin arzikin duniya na kashi biyu da rabi cikin 100, a shekarar bana, sabanin ha sashen kashi uku da rabid a aka yi a baya.Rahotan yace, tattalin arzikin duniya ya shiga cikin mawuyacin hali, abinda ke barazanar jefa kasahen duniyar cikin halin kakanikayi, kamar yadda aka gani a shekarar 2008, sakamakon durkushewar Bankin Lehman.Bankin yace, kasashen da suka fi habakar tattalin arziki, ba zasu iya dogaro ga kasuwanni ba wajen biyan bashinsu, inda yayi gargadin cewar matsalar na iya shafar bankuna da hukumomin kudi masu zaman kansu.Bankin ya bukaci kasashe masu tasowa da suyi nazarin halin da suke ciki, dan kaucewa abinda kan je ya dawo, ganin yadda matsalar ta fara shafar kasashe irinsu India, Brazil, Russia, Afrika ta kudu da Turkiya.. 

Bankin duniya
Bankin duniya
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.