Isa ga babban shafi
Najeriya

El Rufai ya yi kira na a rushe kamfanin NNPC a Najeriya

A Nigeria, Gwamnan Jahar Kaduna Nasir El-Rufai, ya yi kira ga shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya gaggauta rushe kamfanin man fetur na kasar wato NNPC.

Motar dakon man NNPC.
Motar dakon man NNPC. Getty Images/Suzanne Plunkett
Talla

 

Gwamna El-Rufai yace cin hanci da rashawa da suka yi katutu a kamfanin ne ya sa shi yin wannan kiran.

Cikin fushi, gwamnan yace anan gudanar da kamfanin man ne tamkar wata gwamnati mai zaman kanta, inda ya bayyana fatan ganin shugaba Muhammadu Buhari ya Rusa kamfanin, tare da kirkiro sabo, domin a cewar shi in har aka gagara Rusa shi to fa kamfanin na NNPC zai iya kashe Nigeria.

Gwamnan ya kara da cewa akwai wasu ma’aikatan kamfani su kasa da dubu daya da ke cin karen su ba babbaka da dukiyar kasar, inda a cewar shi cikin shekaru 3, suke mika wa hukumomi kashi 42 cikin 100 kawai na abinda ya kamata a sanya a asusun Gwamnatin Tarayyar kasar.

Badakalar cin hanci da rashawa dai a kasar ya dabaibaye kanfanin man fetur din, abinda ke ci gaba da janyo wa tattalin arzikin kasar koma baya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.