Isa ga babban shafi
Najeriya - Faransa

Buhari zai halarci taron tattalin arzikin kasashen Afrika a Paris

Shugaban Najeriya Muhd Buhari zai yi tattaki zuwa Faransa a yau Lahadi, inda zai shafe kwanaki 4, domin halartar taron tattalin arziki tsakanin kasar ta Faransa da kasashen Afrika.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Carlo Allegri
Talla

Taron wanda zai gudana a karkashin jagorancin shugaban Faransa Emmanuel Macron, zai maida hankali kan batutuwan da suka hada da, makomar basukan da ake bin kasashen Afrika, kudaden tallafin da kasashen Turai ke ba su da kuma tattaunawa kan shirin yiwa fannin tafiyar da kamfanoni masu zaman kansu da kananan sana’o’i garambawul.

Baya ga batun na tattalin arziki ana sa ran shugaban Najeriyar zai gana da takwaransa na Faransa kan karuwar hare-haren ta’addanci a yankin Sahel da kuma zagayen Tafkin Chadi, batun sauyin yanayi da kuma alakar Diflomasiya.

Tasirin annobar Korona da kuma matsalolin tsaro na hare-haren ‘yan bindiga da na kungiyoyin ‘yan ta’adda na daga cikin dalilan da suka haifar da nakasu ga cigaban tattalin arzikin wasu kasashen nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.