Isa ga babban shafi
Tattalin Arziki

Kasashe matalauta suna biyan bashi mafi girma cikin shekaru 20 - Kwararru

Kwararru kan tattalin arziki na kasa da kasa, sun yi gargadin cewa yawan kudaden da kasashe masu tasowa ke kashewa wajen biyan bashin da ake binsu yayi hauhawar da ba a taba ganin irinta ba cikin fiye da da shekaru 20 da suka gabata.

Taswirar da ke fayyace hauhawar kudaden da kasashe marasa karfi ke kashewa wajen biyan basukan da ake binsu.
Taswirar da ke fayyace hauhawar kudaden da kasashe marasa karfi ke kashewa wajen biyan basukan da ake binsu. © S&P Global/ Reuters/Marc Jones
Talla

Masu ruwa da tsakin sun kara da cewar, kasashe masu tasowa da dama sun shiga mawuyacin hali sakamakon tabarbarewar da tattalin arzikinsu ya yi a dalilin tasirin barkewar annobar Korona a duniya.

Matsalar tattalin arzikin kasashen masu tasowa kuma ta yi kamari ne, a yayin da kuma shirin rangwame na dakatar da biyan bashin da suke yi wanda ke karkashin kasashe masu hannu da shuni ke shirin karewa.

A farkon wannan watan Bankin Duniya ya ce tasirin annobar Korona ya bar kusan kashi 60% na kasashe masu karamin karfi a cikin hatsarin bashi.

Rahoton Cibiyar nemawa kasashe masu tasowa ‘yanci daga bautar biyan basuka na rashin adalci ya nuna cewa biyan bashin kasashe masu tasowa ya karu da kashi 120 cikin 100 tsakanin shekarar 2010 zuwa 2021, wanda ya kai matakin da ya fi girma tun daga shekarar 2001.

A duniya baki daya, kasashe 54 a halin yanzu ke cikin rikicin basussuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.