Isa ga babban shafi

Za a kafa sabon asusun taimaka wa kasashe matalauta

Bankin Duniya na shirin kafa asusun gaggawa na Dala biliyann 170 domin taimaka wa kasashe matalauta da ke fama da tarin matsaloli.

Shugaban Bankin Duniya, David Malpass
Shugaban Bankin Duniya, David Malpass AP - Jose Luis Magana
Talla

Shugaban Bankin Duniyar David Malpas ya bayyana cewa, za su ci gaba da aikin da suka faro lokacin barkewar annobar Korona da aka kafa makamancin wannan asusun domin agaza wa kasashen da ke fama da tsadar farashin kayayyakin masarufi, matsalar da ta kara yin kamari a baya-bayan nan sakamakon mamayar Rasha a Ukraine da kuma karancin kudi saboda basuka.

Malpass ya ce, tarin basuka da kuma tashin farashin kayayaki na a matsayin manyan matsaloli guda biyu da ke barazana ga habbakar tatttalin arzikin duniya.

Shugaban Bankin Duniyar ya ce, yana cikin damuwa kan halin da kasashe masu tasowa ke ciki, inda suke fuskantar tsadar farashin makamashi da taki da kuma abinci.

A makon jiya ne, Bankin Duniyar mai cibiya a birnin Washington ya rage hasashensa na habbakar tattalin arzikin duniya a bana, yayin da shi ma asusun Lamuni na IMF ake sa ran zai rage nasa hasashen a wannan Talatar.

Malpass ya ce, asusun gaggawar na tsawon watanni 15, zai ci gaba da wanzuwa har zuwa  Yunin shekarar 2023, inda kuma zai maye gurbin asusun rage radadin tasirin annobar Covid-19 da zai kawo karshe a watan  Yunin bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.