Isa ga babban shafi

Ma’aikatar kudi ba ta san da shirye-shiryen canza fasalin kudin Najeriya ba -Zainab Ahmed

Ministar kudin Najeriya,Zainab Ahmed, ta yi fatali da shirin babban bankin Najeriya (CBN) na sake fasalin wasu takardun kudi na Naira.

Shirin sake fasalin takardun kudi 100, 200, 500 da 1,000
Shirin sake fasalin takardun kudi 100, 200, 500 da 1,000 © AFP - Pius Utomi Ekpei
Talla

Zainab Ahmed ta ce ma’aikatar ba ta san da shirye-shiryen ba, ta hanyar kafafen yada labarai ne kawai ta samu wannan labari.

Ministar na fadar  haka ne a jiya Juma’a lokacin da ta bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa kan harakokin kudi domin zaman kare kasafin kudin ma’aikatar.

Kalaman nata na zuwa ne sa’o’i 48 bayan Gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana shirin sake fasalin takardun kudi 100, 200, 500 da 1,000 a watan Disamba.

Ana shirin sake fasalin N100, N200, N500, da N1000 sannan a fara rarrabawa a watan Disamba sannan a ranar 31 ga Janairu, 2023, ana sa ran za a daina aiki da tsofaffin takardun kudi.

Godwin Emefiele ya ce an dauki matakin ne da nufin ganin an shawo kan kudaden da ke yawo a kasuwanni, da skawo karshen hauhawar farashin kayayyaki, da kuma magance jabun kayayyaki. Godwin Emefiele ya ce sarrafa kudaden ya fuskanci kalubale da dama .

A cewar babban gwamnan bankin Najeriya Godwin Emefiele, Shugaban kasar Mohamadu Buhari na sane da wannan tasri,ya kuma bayar da amincewarsa a kai.

Kakakin babban bankin Najeriya Nwanisobi ya bayyana kwarin gwiwar cewa, yin haka zai taimakawa wajen dakile al’amuran ta’addanci da sace-sacen mutane ta hanyar samun makudan kudade da suke wajen tsarin banki da ake amfani da su a matsayin hanyar samun kudin fansa.

Don haka Nwanisobi ya bukaci ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da matsayinsu ba, da su goyi bayan aikin sake fasalin Naira, domin yana da amfani ga tattalin arzikin kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.