Isa ga babban shafi
Turai

Turai- an fara zirga zirgan jiragen sama

Filayen jiragen saman kasashen Turai sun fara barin jiragen sama tashi da sauka acikinsu, tun bayan dakatar da harkoki kusan mako daya saboda matsalar yanayi.Matafiya ta jiragen sama akasashen Turai sun fuskanci matsaloli da dama na rashin samun jiragen sama zuwa wurarenda suke bukata, saboda matsalar  gurbacewar sararin samaniya, saboda yadda hayaki daga wagegen  rami daga tsaunukan kasar Iceland

Talla

Aman wuta daga tsaunukan Iceland ne dai ya haifar da tsaida harkokin sufurin sama akasashen Turai, saboda bazuwar bakin hayaki sararin sama.

Filayen jiragen Sama na kasashen Italiya, Switzerland da Faransa sun dawo da tashi da saukan jirage yau Talata, koda shike an soke tashin jirage da dama ayau din.

Kasar Hungary ta maida dukkan harkokin zirga zirgan jiragen saman ta zuwa wurare.

A kasar Poland wadda ta bude tashoshin jiragen saman ta hudu tun ajiya, ta rufe su ayau.

Kasar Germus tace sai da yammacin yau ne zata bude nata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.