Isa ga babban shafi
Turai

An samu faduwar hannaye jarin Nahiyar Turai

Hannayen Jari a kasashen Turai yau sun durkushe, sakamakon mumunar faduwar hannun jarin kasar Japan, mai fama da matsalar girgizar kasa da kuma igiyar ruwan tsunami.A kasar ta Japan, hannayen jarin sun fadi da sama da kashi 10, abinda ya dada jefa tattalin arzikin kasar cikin halin kakanikayi, sakamakon bala’in da ya aukawa kasar, wanda ya lakume rayuka akalla 10,000.A kasar Jamus, hannun jarin kasar, mai suna DAX, ya fadi da kashi hudu da rabi, yayin da aka samu faduwar hanayen jarin sama da kashi uku a biranen London, Milan da Paris.Rahotanni sun nuna cewar, kanfanon samar da makamashi dake da nasaba da nukiliya, kamar su Areva, EDF, da EON sun samu koma baya sosai, wajen hada hadar su, ganin yadda hanayen jarinsu suka fadi warwas.Masana harkokin tattalin arziki sun bayyana cewar, asarar da ta shafi kasar Japan, ta zarce ta Dala biliyan 35. 

Reuters/Bogdan Cristel
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.