Faransa
A gano daya daga cikin bakaken akwatinan jirgin kanfanin Air France da yayi hadari
Masu bincike, sun gano daya daga cikin bakaken akwatinan jirgin saman kamfanin Air France, wanda ya yi hadari kan tekun Atlantic cikin shekara ta 2009.Masu bincike sun bayyana gano bakin akwatin na wannan jirgin da yayi hadari bayan tasowa daga garin Rio de Janeiro kan hanyar shi zuwa Paris babban birnin kasar Faransa. Kuma babu wanda ya tsira daga hadarin.
Wallafawa ranar: