Isa ga babban shafi
Turkiya

Taron kasar Turkiya kan taimakon kasashe matalauta

Shuwagabannin kasashen matalauta na duniya 48 tare da na kasashen da ke bada tallafi, hukumomin kasa da kasa na ci gaba da zaman taronsu a birnin Istanbul na kasar Turkiya karkashin jagorancin Sakatare Janar na Majalasar Dumkn Duniya Ban Ki Moon.      Ba a bukatar sadaka ! zuba jari ake bukata !waanan su ne kalaman Sakataren Majalasar Dumkin Duniya Ban Ki Moon. Domin zuba jari a cikin kasashen zai taimaka wajen kara habbaka tattalin arziki tare da samun daidaito a duniya, wanda zai ba al’ummomin kasashe matalauta damar cin moriyar kasashensu.Har ila yau, Majalasar Dumkin Duniya ta bayyana samar da wasu matakai da za su bata damar bin diddigin alkawulan da kasashe masu karfin arziki na duniya suka yi wajen tallafawa kasashe matalauta.Ban Ki Moon ya bayyana cewa, a baya kasashen masu kumbar susa sun dauki alkawulla masu yawa amma daga baya basu cika su ba, akan haka ne daga yanzu majalisar dinkin duniyar zata zage damtse wajen bin diddigin alkawulan da kasashen masu arziki suka yiwa matalautaHar ila yau babban magatakar na Majalasar Dumkin Duniya Ban Ki Moon ya tabo wasu fannoni masu matukar muhimmanci wajen tallafawa kasashen matalauta da al’ummominsu ke rayuwa da kasa da dalar Amruka 745 a shekara wadanda yawansu ya tasarma miliyan 900 kwatankwacin 12% na al’ummar duniya. Dan haka yana da matukar muhimmanci kasashen matalauta su kara bukasa shianin noma wanda zai samar da aikin yi ga kimanin kashi 70% na jama’ar su.A lokacin da ya karbi jawabi shugaban kasar Iran Mohmud Ahmadi Nijad ya zargi kasashen masu hannu da shuni, da hana ci gaban arziki a cikin kasashen matalauta, wanda ya ce tsarin mulkin mallaka ne ya haifar da shi.  

Taron kasashen duniya domin taimakama kasashe matalauta
Taron kasashen duniya domin taimakama kasashe matalauta
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.