Isa ga babban shafi
Italiya

Silvio Berlusconi da zaben tarihi a Italiya

Jama’iyar Silvio Berlusconi ta bangaren dama a kasar Italiya , ta yi ragon-kaya , inda ta sha kaye a zaben hukumomi da ya gudana a cikin kasar.A yankin Milan ,shiyar da Silvio Berlusconi ke tunkafo da shi daga cikin kuri’u na muzabu 1195 da aka kilga daga yawan muzabu 1251 da yankin ya kumsa ,dan takara na bangaren hagum Giuliano Pisapia na kan gaba da kishi 55 da digo 12 cikin 100 , a yayin dad an takara bangaren dama Letizia Moratti na jama’iyar PDL Peuple de la Liberte na Sivio Berlusconi ya samu kishi 44 da digo 87 cikin 100.Shiryar Milan it ace babbar cibiyar tattalin arzikin da kassuwanci na kasar Italiya inda kuma anna ne a ka haifi Silvio Berlusconi wurin da kuma ya ke lashe zabe duk shekara ba tare da wata tantama ba har tsawonshekaru 18.Wanan jama’iya ta sha kaye a yankin Naples ,in da bayan samun sakamako na mazabu 750 cikin 886 jama’iyar hagunm na da kishi 65 da digo 19 a yayin da jama’iyar Silvio Berlusconi ta bangaren dama ked a kishi 34 da digo 80 cikin dari.Jama’a na danganta sakamakon wanna zabe , da ban kashi da kadangare ke ba damo,wanda kuma ga dukan alamu ke shirin kawo canji a cikin siyasar kasar Italiya 

Silvio Berlusconi na Italiya
Silvio Berlusconi na Italiya REUTERS/Bogdan Cristel
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.