Isa ga babban shafi
FARANSA

Tattalin arzikin Faransa ya nuna alamar tabarbarewa

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya katse hutunsa a yau Laraba domin gudanar da wani taron gaggawa kan farfado da tattalin arzikin kasashen duniya. A dai dai lokacin da kuma tattalin arzikin Faransa ke nuna alamar tabarbarewa.Sarkozy hadi da sauran shuwagabannin kasashen turai na cikin matsin labba a dai dai lokacin da suke gudanar da hutunsu kuma tattalin arzikin duniya ke fuskantar barazana.A kasar Faransa ayyukan masana’antu sun fadi da kashi 1.9 a watan Juni,A yau laraba ne shugaban Sarkozy zai gana da Prime Ministansa wanda ya katse hutunsa da yake gudanarwa a kasar Itali, shugaban kuma zai gana da Ministan kasasfin kudin Faransa tare da shugaban babban bankin kasar.  

Shugaban Kasar Faransa Nicholas Sarkozy
Shugaban Kasar Faransa Nicholas Sarkozy Reuters/Philippe Wojazer
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.