Isa ga babban shafi
EU

Kotu ta Halarta kudaden Tallafin kasashen Turai

Wata Kotu a kasar Jamus, ta halarta tallafin kudaden da ake baiwa kasashen Turai, amma ta bukaci Yan Majalisu su dinga sanya baki a ciki, maimakon gwamnatoci su dinga gaban kansu.A wani gagarumin hukunci da aka bayar yau, kotun fassara kundin tsarin mulkin da ke Karlsruhe, a Jamus, tace duk wani tallafi da za’a bayar nan gaba, sai an samu amincewar Yan Majalisun kasahsen Turai.Mai shari’a Andreas Vosskuhle, ya bukaci shugabanin kasashen Turan, da su dinga samun amincewar Majalisar.Wannan mataki ya daga darajar kudin Euro, wanda ta samu koma baya sakamakon tsoron ko kotun zata haramta bada tallafin.Har ila yau, matakin na zuwa ne a dai dai lokacin da Yan Majalisun kasashen Faransa, Italy da Spain, ke kada kuri’a don amincewa da matakan tsuke bakin aljihu, da kuma basukan kasashen Turai. 

Uwar gida Angela Merkel ta kasar Jamus
Uwar gida Angela Merkel ta kasar Jamus
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.