Isa ga babban shafi
Venezuela

Chavez ya soki kasashen Yammaci

Shugaban Kasar Venezuela, Hugo Chavez, ya soki kasashen Yammaci da haddasa yake yaken da ake samu, da wasu yake yaken da Yan mulkin mallaka zasu kaddamar a duniya, wanda aka fara da kasar Libya.Wata wasika da shugaban ya rubuta, ya nemi bayani kan yadda Amurka ke kokarin mamaye duniya, wajen girke dakarun ta a ko’ina. Shugaba Chavez yace yake yaken sun wuce gona da iri wajen kutsa kai cikin kasashen duniya dake da ‘Yancin kansu, da kuma kawar da kai da Majalisar Dinkin Duniya ke yi.Shugaba Chavez yace mamaye Libya, wani mataki ne na sace arzikin man kasar, shugaban kuma ya bayyana nuna goyan bayansa na samun kasar Palasdinu. 

Shugaban Kasar Venezuela Hugo Chavez
Shugaban Kasar Venezuela Hugo Chavez
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.