Hannayen jarin Turai sun tashi bayan Jamus ta amince sake ceto Tattalin arzikin Turai
Kasuwannin hannayen jarin turai sun tashi sama bayan da Majalisar dokokin kasar Jamus ta amince da shirin fadada karfin Kungiyar Tarayyar Turai kan asusun tallafawa matsalar tattalin arziki.Kada kuri’ar ta zama gwaji ga Shugaban gwamnatin kasar Angela Merkel, yayin da wasu da ke cikin gwamnatin hadakar suka yi adawa da tsarin.Yan majalisa 523 suka amince da tsarin, 85 suka kada kuri’ar adawa, uku basu jefa kuria ba, yayin da tara suka kauracewa zaman majalisar mai wakilai 620.A kasar Girka mai fama da matsalar tattalin arziki, an gudanar da zanga zanga, sakamakon ziyarar masu bincike na kasashen duniya kan yiwuwar sake bai wa kasar kudaden tallafi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: