Faransa
Kotu ta mika dukiyar Lilian ga ‘Yar ta
Wata Kotu a Faransa ta sanya kula da dukiyar hamshakiyar Attajirar kasar, Lilian Bettencourt, a hannun ‘Yar ta, da jikokinta , saboda abinda suka kira tabarbarewar lafiya da kuma dimbin shekaru.Kotun tace, daga yanzu, Francoise, da kuma jikokin ta zasu dinga tafiyar da dukiyar da ta kai Euro biliyan 16, abinda lauyanta yace bai amince ba, kuma zai daukaka kara.Ita Lilian Bettencourt ta na da shekaru 88, kuma sun dade suna takaddama da yar, kan yadda ta ke yin kyauta dukiyarta ta fitar hankali, abinda Yar ke cewa, wani shiri ne na rabe dukiyar.
Wallafawa ranar: