Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

Tarayyar Turai zata biya kamfanin Renault kudi domin biyan ma’aikata

Majalisar Wakilan Kasashen Turai sun amince da biyan kudaden da suka kai kudin Euro miliyan 25.5 ga ma’aikatan da kamfanin kera motoci kirar Renault na Faransa ya kora daga aiki. Ma’aikatan sun kai 3,500 da aka dakatar dasu tun shekaru biyu da suka gabata. 

Kamfanin Kera motocin kasar FaransaRenault
Kamfanin Kera motocin kasar FaransaRenault Sean Gallup/Getty Images
Talla

A wancan lokaci an zabtaresu ne saboda komadan tattalin arziki da kamfanin kera motocin na Renault ya shiga.

Asusu na musamman da Kungiyar Turai ta bude, ta wadata kamfanin da kudin da ya kai Euro Miliyan 500 domin biyan ma’aikatan hakkin su idan har an yi tankade da rairaya saboda matsaloli da kamfani ke fuskanta.

Da farko Kungiyar Turai ta ki amincewa da bukatar biyan ma’aikatan saboda sabani da aka samu tsakanin Gwamnatin Faransa da Kungiyoyin Kwadago, game da Karin wa’adin ajiye aiki daga shekaru 60 zuwa shekaru 62.

Kudaden da ake bai wa ma’aikatan da aka dakatarwa zasu taimaka ne wajen neman wani aikin, ko koyon sana’o’i da zai tallafawa bukatun mutunen.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.