Isa ga babban shafi
Rasha

Kasashen duniya na dari-dari kan zaben kasar Rasha

KASASHEN Duniya na dari dari wajen mika sakon taya murna game da zababen shugaban kasar Russia, Vladimir Putin, yayin da Yan adawar kasar suka kira wata zanga zanga yau. Shugaban Kasar China, Hu Jintao, shine shugaba na farko da ya aike da sakon taya murna ga Vladimir Pitin, sakamakon nasarar da ya samu, na kashi 64 cikin 100 na kuri’un da aka kada, amma Britaniya tace tana jiran rahotan masu sa ido daga kungiyar kasashen Turai, tare da hukumar kare Hakkin Bil Adama kafin ta bayyana matsayin ta.Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Britaniya, yace suna goyan bayan ganin demokradiya ta zauna a Russia kamar kowacce kasa, kuma Russia na da hakkin tabbatar da kare hakkokin dan Adam.Dangantaka tsakanin kasashen Britaniya da Russia tayi tsami a Yan shekarun nan.Kaasshen Amurka, Jamus, da Faransa, basu ce komai ba dangane da zaben, yayin da Yan adawar kasar ke gangami dan nuna rashin amincewar su da zaben.Lokacin da yake jawabin, bayan nasarar da ya samu, shugaba Putin cikin hawaye, yace, sun baiwa marada kunya wajen gudanar da karbaben zabe, da kuma samun nasara. 

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.