Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy mai barin gado ya ce a natsawa Hollande domin ya kada shi

Bayan yakin dubaru, yanzu haka shugaban kasar Fransa mai barin Gado Nicolas Sarkozy ya kirkiro da sabuwar dubarar tunzura magoya bayan abokin takararsa Francois Hollande ta hanyar zarginsa da gujewa mahawara, bayan kafin a gudanar da zagaye na farko na zaben Hollande din ya bayyana cewa a zai shiga mahawarar.Jaridar le Figaro ta yan mazan jiya ta ruwaito wani mashawarcin shugaban mai barin gado Nicolas Sorkozy na cewa, za su shiga yakin neman zaben zagaye na 2 da za’a yi a ranar 6 ga watan mayun gobe, da runtsen ido ne, tare da yi amfani da duk wata hanyar da ta tari gabansu, domin hana abokin hamayar tasu cin nasara.Jaridar ta le Figaro ta kara da cewa, shugaba Sarkozy ya nemi magoya bayansa da cewa, su ci gaba da matsawa abokin takararsa Francois Hollande Lamba, kamar yadda yake matsa masa lamba. 

© AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.