Isa ga babban shafi
Spain

Gwamnatin kasar Spaniya ta dauki wasu sabin matakan tafiyar da bankunan kasar

Gwamnatin kasar Spain a yau juma’a ta amince da wani sabon shirin tafiyar da bankunan kasar da suka fi karkata kan sashen gidaje, inda aka umarci bankunan da su bayyana sakamakon ayukansu, da kuma umartarsu da samar da wani sabon shiri na kimanin Euro miliyan dubu 30 nan gaba.Kakakin gwamnatin kasar ta Spaniya Soraya Saenz de Santamaria bayan taron majalisar ministocin a yau, ya bayyana cewa, wannan sabon shirin zai bada damar samun haske kan yadda bankunan kasar ta Spaniya ke tafiyar da ayukansu da kuma kara masu inganci, domin kaucewa fadawarsu cikin matsalar tattalin arziki.  

L'Etat espagnol sera actionnaire de Bankia a hauteur de 45%.
L'Etat espagnol sera actionnaire de Bankia a hauteur de 45%. REUTERS/Paul Hanna
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.