Girka-EU-IMF
Gwamnatin rikon kwaryar kasar Girka ta fara aiki a yau
A kasar Girka yau Gwamnatin riko ta fara aiki domin shirya zabe cikin makonni 6 masu zuwa, bayan zaben da aka yi ba a kamala ba, na ranar 6 ga watan 5, yayin da ake samun zullumin yadda batun kudaden Euro za su kasance a kasar Spain da Italia.Zaben dake tafe a Girka ranar 17 ga watan gobe, babu tabbatas cewa, za a sami Gwamnati da zata iya aiwatar da tsarin ceton kudaden euro kamar yadda kungiyar kasashen Turai da kuma Asusun bada lamuni na duniya IMF suka tsara.
Wallafawa ranar: