Kotun Libya ta yanke wa wasu Turawa hukuncin dauri a gidan yari
Wata kotun Soji a kasar Libya ta yankewa wasu Turawan Ukraine 19 da wasu uku ‘yan kasar Belerus da Biyu ‘Yan Rasha hukuncin dauri a gidan yari bayan kama su da laifin zama Sojojin haya na Kanal Gaddafi a rikicin kasar.
Wallafawa ranar:
Daga cikinsu Turawan, an yankewa wani Dan Rasha hukuncin daurin Rai-da Rai a gidan yari sauran kuma aka yanke masu hukuncin daurin shekaru 10.
Sai dai dukkanin Turawan sun musanta zargin da kotun ke masu inda suka ce su ma’aikata da ke aiki a bangaren man fetir.
A zaman kotun, Akwai jakadun kasashen Ukraine da Belarus wadanda suka ce zasu daukaka kara.
Wani kakakin gwamnatin Libya yace tun Ogustan bara ne aka cafke Turawan a birnin Tripoli.
Akwai dai hulda tsakanin gwamnatin Ukraine da Gaddafi, kuma an kiyasta akwai kimanin ‘Yan kasar Ukriane 1,500 da ke zama a Libya kafin barkewa rikici a tsakiyar Febrairun shekarar 2011.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu