Isa ga babban shafi
Fransa

Barayin agogo sun addabi kasar Faransa

Jami’an tsaro a kasar Faransa na farautar wasu gungun barayi da su ka kware wajen satan agoguna masu tsada a hanun mutane.Akalla sun saci agoguna na fiye da Euro Miliyan a makwanni biyu da su ka wuce, kamar yadda Kamfanin Dillancin labaran AFP ya rawaito. 

Hoton wani agogo mai tsada da barayin kan hara
Hoton wani agogo mai tsada da barayin kan hara Forbes.com
Talla

Barayin sukan sa ido su ga wake sanye da agogo mai tsada kana sai su bishi zuwa motarsa a inda daya daga cikinsu akan babur zai bige madubin duba baya na motar.

A yayin da mai motar ya yi yunkurin gyara madubin duba bayan sai wani na biyu akan babur ya taho ya sabule agogon.

Jami’an tsaron na kyautata zaton cewa barayin daga Birnin Naples da ke kasar Italia su ke inda ake fama da irin wannan satar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.