Isa ga babban shafi
Birtaniya

Gwamnatin Assad ta banu, inji Hague

Sakataren Harkokin wajen kasar Birtaniya, William Hague, ya ce kasar gwamnatin shugaba Bashar al- Assad ta shiga wani halin kakani kayi, kuma bai kamata ta cigaba da kasancewa. Hague ya fadi hakan ne a lokaci da ya kai wata ziyara kasar Iraqi, inda ya kara da zargin cewa kasar Iran na tallafawa gwamnatin Assad, a yayin da rikicin na Syria ya koma yakin basasa.  

Sakataren Harkokin wajen kasar Birtaniya, William Hague
Sakataren Harkokin wajen kasar Birtaniya, William Hague REUTERS/Kham
Talla

“Mun yi ammanna cewa gwamnatin Bashar al- Assad ta shi ga uku, domin zai yi wuya ta cigaba da kasancewa, domin an tafka laifuka da dama da bai kamata gwamnatin ta cigaba da kasancewa ba.” Hague ya ce a lokacin da ya ke bayani a wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da takwaransa, Hoshyar Zebari.

Ya kara da cewa “Mun yi amanna da kafa gwamnatin wucin gadi, wanda yin hakan zai iya kawo zaman lafiya a kasar ta Syria.”

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.