Isa ga babban shafi
Faransa

Gobe Hollande zai gabatar da kasafin kudin badi

Gobe ake sa ran shugaban kasar Faransa, Francois Hollande, zai gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa, abinda ake ganin zai tabbatar da aniyarsa ta zaftare kashe kudaden jama’a. 

Shugaban kasar Faransa, François Hollande
Shugaban kasar Faransa, François Hollande REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Kasafin wanda shine na farko da shugaban zai gabatar, tun bayan zabensa a watan Mayu, zai kunshi Karin haraji ga masu hannu da shuni, kamar yadda ya bayayan lokacin yakin neman zabensa, da kuma rage gibin kasafin kudi.

Akalla gwamnatin Hollande na bukatar rage euro biliyan 30 a cikin shekara mai zuwa.

A wani bangare kuma, a kasarta Faransa, yawan marasa aikin ya harba kamar yadda ministan kwadago kasar Michel Spain, ya sanar ,duk da yunkurin da gwamnatin Shugaba Hollande ke yi, na ganin cewar an samarwa matasa aikin yi a cikin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.