Isa ga babban shafi
Faransa

Ana zargin gwamnatin Faransa da hanu kashe Ghaddafi

Yanzu haka wata takaddama ta kaure kan zargin da akewa Gwamnatin Faransa, a karkashin jagorancin Tsohon shugaban kasa, Nicolas Sarkozy, da hannu wajen kashe shugaban kasar Libya, Muammar Ghaddafi, saboda kada ya fallasa kudaden da ya ba Sarkozy domin yakin neman zabe.

Tsohon shugana kasar Faransa, Nicholas Sarkozy da tsohon shugaban kasar Libya, Moammar Ghaddafi
Tsohon shugana kasar Faransa, Nicholas Sarkozy da tsohon shugaban kasar Libya, Moammar Ghaddafi 1.bp.blogspot.com
Talla

Wannan ya biyo bayan zargin da Mahmoud Jibril, shugaban gwamnatin rikon kwaryar Libya yayi, na cewar jami’an kasar Faransa ne suka kashe Ghadafin.

Ikrarin tsohon shugaban rikon kwaryar libya, Mahmud Jibril cewar, dakarun kasar Faransa ne suka shiga cikin ‘Yan juyin juya halin Libya, kuma suka kashe Tsohon shugaban kasa, Muamar Ghaddafi, yanzu haka ya janyo kace nace.

Jibril yace, shugaba Bashar al Assad na Syria ne ya sayarwa da Faransa bayanna sirri kan Ghadafi, wanda akayi amfani da su wajen kashe shugaban.

Jaridar kasar Italia, Corriere della Sera, ta jiyo wani babban jami’in diplomasiyasar kasahsen Turai na cewar, inda har yan kasashen waje ne suka kashe tsohon shugaban na Libya, to babu tantama daga Faransa suke.

Jami’in yace, shugaban Faransa na wancan lokaci, Nicolas Sarkozy, ya kekashe kasa dole sai a hambarar da gwamnatin Ghaddafi, saboda zargin da yayi na bashi makudan kudade dan gudanar da yakin neman zabe a shekarar 2007.

A wani bangare kuma, Jaridar Daily Telegraph ta Britaniya, ta ruwaito wani baban jami’in tsaron ‘Yan Tawayen Libya, Rami el-Obeidi, na cewa Syria ce ta sayarwa da Faransa lambar wayar Ghaddafi, wanda jami’an tsaron Faransa sukayi amfani dashi wajen gano inda yake.

Jami’in yace, shugaba Bashar al Assad ya bada hadin kai da Faransa ne,da zummar cewar za ta taimaka masa tsira da gwamnatinsa.

Obeidi ya kara da cewar, kama shugaba Ghaddafi da kuma kashe shi, wannan shiri ne kawai na kasar Faransa.

Amma wani masanin harkokin tsaron Faransa, Eric Denece yayi watsi da wanan zargi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.