Isa ga babban shafi
Girka

An tsaurara matakan tsaro a Girka saboda ziyarar Merkel

A yanzu haka a tsaurara matakan tsaro a kasar Girka, a yayin da ake sa ran Shugabar kasar Jamus, Angela Merkel, za ta ziyarci kasar. Tsaurara matakan tsaron na nasaba da yunkurin dakile boren da ake tsammanin mutane za su gudanar saboda alakanta shugabar da matakan tsuke aljihun baki da kasashen Nahiyar Turai ke yi.

Masu Bore da 'Yan sanda, a wata zanga zanga da aka gudanar a Girka
Masu Bore da 'Yan sanda, a wata zanga zanga da aka gudanar a Girka rfi
Talla

Akalla ‘Yan sanda, 6,500 tare da tankunan da kuma jairage masu saukan angulu za a ajiye a layika a gobe, inda hukumomi su ka bayyana cewa za a rufe tsakiyar birinin Athens.

A lokacin ziyarar, za a dauki matakan tsaro na musamman akan Ofishin jakadincin Jamus dake Girka da kuma sauran gina gine mallakar kasar, a cewar Kamfanin Dillancin labaran kasar.

Shugaban kasar, Antonis Samaras, ya tabbatarwa Merkel, cewa ana maraba da zuwan nata, a yayin da wasu dayawa a kasar su ke nuna kinsu ga ziyarar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.