Mutane 400,000 ke mutuwa ta dalilin taba a Rasha duk shekara, inji Medvedev
Hukumomi a kasar Rasha sun ce zasu dauki wani matakin da zai rage mashaya taba a kasar, domin ganin cewa an rage rabin mashaya taban kasar. Firaministan kasar, Dmitry Medvedev ya bayyana hakan, inda ya nuna rashin jin dadinsa saboda Rasha a shekarun da suka gabata, bata dauki matakan rage shan taba ba, wanda hakan ya sa ta zamo kasa ta biyu da aka fi shan taba bayan China a duniya.
Wallafawa ranar:
A cewarsa, yawan mata masu shan taba ya karu da kashi 22 a farkon shekarun 1990’s, a yayin da yawan masu shan farko ya karu da kashi 11.
Hukumar kula da kiwon lafiya ta kasar ta shirya wani daftarin kudirin doka da zai haramta shan taba a wuraren da jama’a su ke, musamman a mashaya, kamar yadda Firaministan ya fada.
Akalla mutane miliyan 44 ‘Yan kasar ta Rasha, mashaya taba ne a kullum, inda mafi akasarinsu sun fara shan tabar ne tun su cika shekaru 20, inji Medvedev.
Haka kuma akalla mutane 400,000 ke mutuwa a duk shekara a kasar Rasha ta dalilin cututtuka da suka jibinci shan taba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu