Isa ga babban shafi
Faransa

Kungiyar Amnesty ta nema Faransa da dakatar da koran Romaniyawa

Kungiyar Amnesty ta Duniya ta bukaci Gwamnatin kasar Faransa data dakatar da Koran ‘Yan kasar Romania wanda aka fara tun lokacin tsohon Shugaban kasar, Nicholas Sarkozy. A lokacin mulkin tsohon Shugaban Faransa ne aka yi ta yiwa ‘Yan kasar Romania kwasan karan mahaukaciya ana rusa tantunan ci-rani da suke tsugune a Faransa ana mai dasu kasarsu.  

Wasu 'Yan Romania a kasar Faransa
Wasu 'Yan Romania a kasar Faransa www.sofiaecho.com
Talla

Anyi ta sukan kyamar baki na tsohuwar Gwamnatin domin hatta shi Shugaban Faransa maici, Fransois Hollande, ya nuna baya ra'ayin haka.

Wani rahoton da Kungiyar Amnesty ta fitar a Paris na kiraga jam'iyyar Socialist dake mulki data ga lallai ta soke wancan tsari.

A cewar kungiyar, cikin watanni biyu matsugunan ‘Yan Romania akalla 22 inda mutane akalla 2,300 ke zama, aka rusa. Kuma cikin wadanda aka wulakanta akwai yara kanana 189 .
 

Saboda haka ne Kungiyar tace cigaba da aiwatar da tsarin Koran ‘Yan Romania da Gwamnatin Sarkozy ta fara bai dace gwamnatin Hollande ta cigaba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.