Isa ga babban shafi
Rasha

‘Yan sandan Rasha sun saki masu zanga-zanga 40 a kasar

‘Yan sanda a kasar Rasha sun sako akalla mutane 40, cikinsu harda shugaban ‘Yan adawa, Alexie Navalny bayan kamasu da aka yi a lokacin gudanar da zanga zangar nuna kin jinin gwamnatin Shugaba Vladimir Putin. 

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin REUTERS/Grigory Dukor
Talla

Daruruwan mutane ne suka yi gangami a ranar Asabar din da ta gabata a dandalin Lubyanka, domin tuna cika shekara daya da nuna kin jinin gwamnatin Putin da aka nuna a watan Satumbar day a gabata.

“Duk wadanda aka kama an sako su.” Inji mai Magana da yawun ‘Yan sandan kasar, ba tare da bayar da cikakken bayani ba.

Gwamnatin kasar ta Rasha dai ta yi barazanar cin tarar duk wanda ya gudanar da zanga –zanga, a yayin da shugabannin ‘Yan adawa suka bada umurnin kowa ya halarta a dandalin na Lubyanka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.