Isa ga babban shafi
Faransa

Depardieu ya gurfana gaban Koton Faransa bayan samun izinin zama a Rasha

Fitaccen mai shirin Fina-finan kasar Faransa, Gerard Depardieu, wanda ya samu zinin zama a kasar Rasha daga shugaba Vladimir Putin, ya gurfana a gaban kotu a Paris, akan tuhumar da ake masa na tuki cikin maye. Masu gabatar da kara sun ce, an kama Depardieu ne a watan Nuwamba da ya gabata da laifi lokacin da ya ke tuka babur.

Depardieu Rike da Takardar Shedar Zama kasar Rasha.
Depardieu Rike da Takardar Shedar Zama kasar Rasha. REUTERS/Yulia Chestnova
Talla

Tuni dai Depardieu yace zai koma Rasha dan kaucewa biyan karin harajin da Gwamnatin Faransa ke shirin karawa attajirai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.