Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

Fafaroma Benedict zai yi murabus a Karshen watan Fabrairu

Shugaban Darikar Katolika Fafaroma Benedict na Goma Sha Shida ya ce zai yi murabus a karshen Watan Fabrairu saboda la’akari da yawan shekarunsa. Fafaroma Benedict shi ne mutum na farko da zai ajiye mukamin shugabancin fadar Vatican tsawon shekaru 700.

Shugaban Darikar Katolika Fafaroma Benedict na Goma Sha Shida.
Shugaban Darikar Katolika Fafaroma Benedict na Goma Sha Shida. REUTERS/Alessandro Bianchi
Talla

Bayan bayyana kudirin yin murabus din Fafaroma Benedict wasu sun fara kiran a nada wani daga Afrika a matsayin wanda zai gaje shi saboda yawan mabiya darikar Katolika a Nahiyar.

An kiyasta kashi 15 na mabiya Darikar Katolika cikin Mabiya Biliyan 1.2 ‘Yan Afrika ne, inda adadin ke dada karuwa a kullum.

Cikin mutanen da ke sahun gaba da ake hasashen za su gaji Fafaroma Benedict daga Afrika sun hada da dan kasar Ghana Peter Turkson da ‘Yan Najeriya guda biyu, John Onaiyekan da Francis Arinze.

Fafaroma Benedict sau biyu yana kawo ziyara a Afrika inda ya kawo ziyara a kasar Jamhuriyyar Benin a 2011 bayan ya kai ziyara a kasashen Angola da Kamaru a 2009.

Faparoma mai shekaru 80 dan asalin kasar Jamus, ya bayyana ranar 28 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da zai tube Rigar mulkinsa.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta ce ta mutunta halin da Fafaroma ya ke ciki na tsufa da kasawar jiki, abinda ya kai shi ga daukar wannan mataki.

Shugabannin kasashen nahiyar Turai daban-daban na ci gaba da nuna alhininsu ga kudirin na Benedict.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.