Isa ga babban shafi
EU

Kungiyar Tarrayyar Turai ta nemi mambobinta da su samar da ababan more rayuwa ga jama’arsu

Kungiyar Tarayyar Turai, ta nemi membobin ta su samar da ababen more rayuwa ga jama’a, da za su saukaka musu lamura, don kawo karshen tayar da kayar baya da ake samu a yankin. Hukumar ta Tarayyar ta Turai ta ce matsalolin tattalin arzikin da ake fusakanta a nahiyar, suna da dama, inda ta zayyana karuwar talauci, banbanci tsakanin masu hannun da shuni da talakawa, da rashin aiki musamman tsakanin matasa.  

Tutocin kasahen Turai
Tutocin kasahen Turai
Talla

kwamishi mai kula da jin dadin jama’a na hukumar Laszlo Andor ya ce burin hukumar shine ganin kasashe sun mayar da hankali kan kula da jama’a, tare da samar da ababan more rayuwa.
 

Andor ya ce in aka zuba jari a kayayyakin more rayuwa a yau, hakan zai taimaka a rage yawan kudaden da za a kashe, don kula da su a nan gaba.
 

Yayin da matsalar bashi ke ci gaba da yin kafar ungulu, ga da ci gaban tattalin arzikin kasashen da ke amfani da kudin Euro, tare da karuwar marasa aikin yi, Gwamnatocin kasashen na EU, sun ci gaba da bullo da hanyoyin matse bakin aljihu, wannan ya sa ake ci gaba da bore a kasashen.

Kuma wasu na ganin wanann na sa lamura na dada tabarbarewa ne kawai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.