Isa ga babban shafi
Bangladesh

Hukumomi a kasar Bangladesh zasuyi karin albashin ma'aikata.

Gwamnatin kasar Bangladesh ta kafa wata hukuma ta musamman domin tsara karawa ma’aikatan kasar albashi, a daidai wani lokaci da dubban ma’aikatan masana’antun kasar ke kokawa da wahalolin da suke fuskanta wajen aiki.

Ma'aikata a kasar Bangladesh
Ma'aikata a kasar Bangladesh REUTERS/Stringer
Talla

Ministan Masana’antu na kasar Abdullatif Siddiqi ya fadawa kamfanin dillancin Labarai na AFP cewa tuni an kaddamar da kwamitin, kuma cikin kwamitin akwai wakilan ma’aikata, da na masana’antu masu zaman kansu.

Wannan mataki da Gwamnatin kasar ta dauka na zuwa ne a wani lokaci da aka sami hasarar rayukan mutane Dubu daya da Dari daya da Ashirin da shida “1,126” wadanda ma’aikatan wata masana’anta ne da ginin ya rusawa a kwanan baya.

A wannan sabon tsarin dai akalla ma’aikacin gwamnatin kasar Bangladesh na iya daukar Albashin Dollar $40 na Amurka ne, karin da Paparoma Pracis ya bayyana da cewar bai taka kara ya karya ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.