Isa ga babban shafi
Faransa

Tsohon PM Faransa Pierre Mauroy ta rasu

Firaministan farko na Jamhuriyar ta biyar Pierre Mauroy ya rasu ya nada shekaru 84.Mauroy ya mutu ne bayan da ya kwashe tsawon rayuwar sa ya na gwagarmaya a jam’iyar Socialiste ta ma su ra’ayin gurguzu na kasar Faransa. Tarihi na nuna cewar a Jamhuriyar ta biyar a lokacin marigayi Shugaba Francois Mitterand, ne Pierre Mauroy ya taka rawar a zo a gani a matsayin shi na Firaministan lokacin.Ya taka rawa kan batutuwa da suka hada mututan ma’aikatan gwamnatin, yin nazari kan lokutan aikin, biyan ma’aikata hakin su daidai wadaida da kuma yin kokarin wajen gani Majalisa dokokin Faransa ta sun amince da kawar da dokar amincewar da hukunci kisa.Ministan harakokin wajen Faransa, Laurent Fabius ya bayanna alhini gwamnatin Shugaba Francois Hollande tareda girmama mamacin.Ya karasa da cewar Pierre Mauroy mutun ne mai son fadin gaskiya tareda mutunta dan Adam.Marigayin ya kuma taba rike mukamin Magajin garin Lille, shekarar 1973.Ya mutu ne bayan da ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya. 

Marigayi Pierre Mauroy
Marigayi Pierre Mauroy Wikimédia
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.