Isa ga babban shafi
Turkey

Turkiya ta yi gargadin yin amfani da karfin Soji domin murkushe masu zanga-zanga

Gwamnatin Turkiya ta yi gargadin yin amfani da karfin Soji domin kawo karshen zanga-zanga da aka kwashe tsawon mako uku ana gudanarwa a Istanbul da sauran manyan biranen kasar.

Kungiyoyin kwadagon Turkiya da suka tsunduma cikin yajin aiki
Kungiyoyin kwadagon Turkiya da suka tsunduma cikin yajin aiki REUTERS/Dado Ruvic
Talla

Mataimakin Firaministan kasar, Bulent Arinc yace gwamnati na iya amfani da karfi ta kowace hanya domin murkushe masu zanga-zangar.

Baza Sojoji dai a saman tituna kan iya hura wutar rikicin da wanda zai kasance babban kalubale ga gwamnatin Jam’iyyar Firaminista Recep Tayyip Erdogan.

Sanarwar gargadin amfani da karfin Soji na zuwa ne a dai dai lokacin da ‘Yan sanda ke ci gaba da harba hayaki mai sa hawaye da ruwan zafi domin tarwatsa masu zanga-zanga a biranen Istanbul da Ankara.

Yanzu haka kuma wasu daga cikin manyan kungiyoyin kwadagon kasar Turkiya, sun yi kiran yajin aikin gama gari , domin adawa da yadda ‘Yan Sanda ke amfani da karfin da ya wuce kima kan masu zanga zanga.

Kakakin kungiyar kwadagon KESK, Baki Cinar, yace daukacin ‘yayan kungiyar da ke Turkiya ne za su shiga yajin aikin, tare da wasu takwarorinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.