Isa ga babban shafi
Faransa

Ana zargin wani tsohon jami'in tsaro Faransa da taimakawa yan Tawayen Rwanda

A kasar Faransa kungiyoyin uku ne ma su zaman kansu suka shigar da kara a gaban  kotun kasar dake Birni Paris kan zargi wani tsohon jami’in tsaro na kasar Paul Barril dangane da batun yaki kasar Rwanda tareda kulla yarjejeniyar taimakawa yan tawayen Rwanda na lokacin wajen kashe yan kabilar Tutsi . 

Alkalai a  kotun kasar  Faransa
Alkalai a kotun kasar Faransa AFP PHOTO / DENIS CHARLET
Talla

Kungiyoyin da suka hada da L’association Survie; la Federation des Ligues des droits de l’homme; da Ligue Francaise des droits de l’homme,
Wadanan kungiyoyin sun tabbatar da cewar suna da hujojin da sheidu kan halakar Paul Barril da yan Tawayen Rwanda daga cikin akoi sabawa dokokin MDD,shi  ne  na  keta doka Hukumar lamba 918 na ranar 17 ga watan Mayu na shekara ta alip 1994 kan batun hana saidawa kasar Rwanda makamai .
Tarihi na nuna cewa Paul Barill ya kasance wani dake hulda da hukumomin Rwanda na lokacin, ya na daya daga cikin wanda da suka lakacin kasar Rwanda.
Paul Barril ya kasance a matsayin sheidu da ya sha bayana a gaban kotun Faransa dangane da batun yaki kare dangi  kasar Rwanda da ya lakume rayukan mutane sama da 800.000 bayan mutuwar Shugaban kasar Juvenal Habyarimana a wani hatsari jirgin sama a shekara ta alip 1994.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.