Isa ga babban shafi
Faransa-Portugal-Bolivia

Faransa-Portugal sun hana jirgin Eva Morales wucewa ta cikin sararin samaniyar su

Hukumomin kasar Bolivia sun bayyana bacin ran su kan yadda aka karkata akalar jirgin dake dauke da shugaban kasar ta, Evo Morales, saboda zargin cewar jirgin na dauke da Edward Snowden da Amurka ke nema ruwa ajallo.

Reuters
Talla

Jim kadan da samun  labarin yiyuwar  kasancewar  Edouard Snoden  cikin  jirgin Shugaban kasar Bolivia, kasashen Faransa da Portugal, sun ki yarda jirgin dake dauke da shugaba Morales, ya wuce ta cikin sararin samaniyar kasar su.
Ministan harkokin wajen Bolivia, David Choquehuanca, ya zargi Amurka da kitsa karyar cewar Snowden na jirgin shugaban.
Ya zuwa yanzu an cima jituwa inda rahotanni ke nuna cewa Faransa ta amince jirgin dake dauke da Shugaba Morales ya wuce ta cikin sararin samaniyar kasar ta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.