Isa ga babban shafi
Turai

Martanin kasashen Duniya game da Juyin Mulkin Masar

Majalisar Dinkin Duniya da kuma kasashen yammacin Duniya sun fara mayar da martani kan kifar da Gwamnatin 'yan Uwa Musulmi ta Mohammed Morsi a kasar Masar, inda suka bukaci gudanar da zabe ba tare da bata lokaci ba

Shugaban kasar Masar. Muhammed Morsi
Shugaban kasar Masar. Muhammed Morsi EUTERS/Asmaa Waguih/Files
Talla

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ko Moon, yace ya fahimci bacin ran 'Yan kasar Masar, amma kuma ya bayyana damuwar sa kan rawar da soji suka taka na sauke Gwamnatin farar hula.

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama, ya bukaci gaggauta komawa mulkin farar hula a Masar, inda ya ke cewa 'Yan kasar Masar ne kawai za su zabawa kansu abinda suke so, tare da bayar da umurnin nazari kan tallafin kudaden da kasar ke bai wa Masar.

Babbar jami’ar diflomasiyar kasashen Turai, Catherine Ashton ta soki yadda aka dinga zubar da jini a kasar, inda ta bukaci bangarorin siyasar kasar da su koma turbar demokradiya.

Ita ma Britaniya ta bayyana juyin mulkin a matsayin abinda ke haifar da fargaba, inda ta bukaci bangarorin su yi taka tsan-tsan.

Kungiyar Amnesty International da Human Rights Watch sun yi Allah wadai da rufe wasu kafofin yada labarai da sojojin suka yi, wanda suka ce ya sabawa Yancin Bil Adama.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.