Minsitocin jam’iyar Berlusconi na kan hanyar janyewa daga cikin gwamnatin Italiya
Tsohon Firaministan kasar Italiya Silvio Berlusconi, ya musanta ikirarin da ake yi na cewa yana da hanu a yunkurin Minsitocin jam’iyar sa na cewa za su janyewa daga cikin gwamnatin kasar.
Wallafawa ranar:
A farkon wannan watan ne kotun kolin kasar Italiya ta yankewa Berlusconi hukuncin daurin talala na tsawon watanni goma sha biyu, lamarin da ya sa ministocin jam'iyar ta Berlusconi suka yi barazanar janyewa daga gwamnatin ta Italiya.
A wata hira da manema labaren kasar, Berlusconi ya nuna damuwa kan yadda za ta kasance ma sa a fagen siyasa, ya ce dole ne Ministocin jam’iyar sa su bada hadin kai.
Yunkurin janyewar Ministocin jam’iyar PDL a kasar ta Italiya a cewar yan jam’iyar PD na bangare Firaminista Enrico Letta barazana ce,
Ya zuwa yanzu Firaministan kasar Enrico Letta bai ce upon ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu