Isa ga babban shafi
Faransa-Birtaniya-Amaruka-Syria

Hollande, Hague da Kerry, a batun cimma matakin na wargaza makamai masu guba a Syria

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya gana a yau da Sakataren Wajen Britaniya Williams Hague da kuma takwaransa na Amirka John Kerry, ida  suka tattauna kan batun kasar Syria.Ganawa tsakani Shugaban Faransa Francois Hollande da John Kerry na Amaruka da William Hague na Birtaniya dai na biyo bayan yarjejeniyar da aka kulla ne tsakanin kasar Amirka da Russia gameda matakan wargaza makamai masu guba da kasar Syria ta mallaka, daya kawo karshen barazanar kai wa Syria hari.

Hague, Kerry da  Fabius a fadar Shugaban Faransa Francois Hollande
Hague, Kerry da Fabius a fadar Shugaban Faransa Francois Hollande Reuters/Michel Euler/Pool
Talla

Gwamnatin kasar Faransa dai na daga cikin wadanda suka tsaya kai da fata cewa matakin soja ne ya dace a kaiwa Syria, domin a ladabtar da Shugaban Syria Bashar Assad saboda amfani da makamai masu guba kan masu adawa da shi ranar 21 ga watan jiya. Lamarin da aka sami mamata masu yawan gaske.
Jim kadan da kamala wanan tautaunawa,kasashen da suka hada da Faransa,Birtaniya,Amaruka na fatar gani an karfafa matsin  lamba zuwa  Gwamnatin Assad, wata hanyar tilasawa hukumomin Syria sauraren bukatun mutanen kasar dama Duniya.

Ministan harakokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius  ya  bukacin  sauren kasashe da su bada hadin kai  domin ceto mutanen Syria, ana  gaba  da  shirya wani zaman taro da yan Adawar kasar Syria a  zauren MDD inji  Laurent Fabius a karshe.   
Jim kadan da kamala wanan tautaunawa na Faransa, hankali mutane ya karkata ne zuwa zauren MDD, idan a yau ne dai ake saran MDD ta karbi rahoton komitin ta na musamman da ta tura Damascus binciko mata zargin amfani da makamai masu guba kan jama’a.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.