Isa ga babban shafi
Faransa

An bayyana sunan Dan bindigan da ya kai hari a ginin Liberation a Paris

Hukumomin Kasar Faransa sun bayyana sunan Dan bindigan da ake zargi ya kai hari ginin Jaridar Liberation da Bankin Societe Generale, a matsayin Abdelhakim Dekhar, wanda aka daure a baya saboda samun sa da hannu wajen aikata laifin kisan kai.

Abdelhakim Dekhar da ake zargi ya kai hare hare a Birnin Paris
Abdelhakim Dekhar da ake zargi ya kai hare hare a Birnin Paris France 2/ Faites entrer l'accusé / Capture d'écran
Talla

Ministan harkokin cikin gidan kasar, Manuel Vals yace gwajin kwayar hallitar da aka yi ya gano cewar Dekhar ne wanda aka kama daren jiya yana kokarin kashe kan sa.

A ranar Laraba ne aka cafke mutumin bayan Jami’an tsaron Faransa sun kaddamar da farautarsa sakamakon harin da aka kai a Ginin Jairidar Liberation a ranar Litinin inda aka harbi wani dan jarida mai daukar hoto.

Dekhar, wanda aka bayyana shekarunsa sun haura 40 an taba kama shi da laifin mallakar Bindigar da aka kai hari a watan Oktoba na 1994 wanda ya yi sanadin mutuwar ‘Yan sanda uku da wani direban Taxi.

Binciken ‘Yan sandan na Faransa ya tabbatar da cewa mutum guda ne ya addabi birnin Paris da hare hare a cikin mako guda, bayan sun gudanar da gwajin jini wanda ya tabbatar da sunan Abdelhakim Dekhar ne ke kai hare haren.

Amma har yanzu Jami’an tsaro ba su bayyana dalilan da ya sa aka kai hare haren ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.