Jamus
Merkel ta amince da kafa gwamnatin hadin kai
Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta amince ta kafa gwamnatin hadin kai da Jam’iyar Social Democrat, watanni biyu bayan nasarar zaben da ta samu.
Wallafawa ranar:
Talla
Jam’iyar CDU ta Merkel, tare da kawar ta Bavarian CSU sun kulla yarjejeniya da SDP bayan sun kwashe sa’oi 17 suna tattaunawa, abinda zai ba su damar kafa gwamnati.
A ranar 17 ga watan Disamba ake sa ran za a sake rantsar da Merkel, sai har yanzu za ta fuskanci matsalolin ciki har da yunkurin samar da katunan mambobi nan da watan mai zuwa domin tabbatar da hadin kan jam’iyun.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu