Isa ga babban shafi
Ukraine

An raunata ‘yan sanda 100 a zanga-zangar kasar Ukrain

Akalla ‘yansanda 100 ne aka raunata, a zanga-zangar da dubban mutane suka yi domin neman a gudanar da zaben gaggawa a kasar Ukraine

wadanda aka raunata a Ukraine
wadanda aka raunata a Ukraine REUTERS/Gleb Garanich
Talla

Dubban mutane ne aka bada labarin sun halarci zanga-zangar inda suke cewa “Juyin-juya hali muke son aiwatarwa a kasarmu” yayin da wasu ke furta kalaman batanci gs shugabannin kasar.

Dukkaninsu a harabar wani makeken Dandali da ke tsakiyar birnin Kiev.

A daidai wannan lokaci ne kuma, wasu dubban mutane suka yi dandanzo a gaban ginin fadar shugaban kasar da kuma wasu manyan cibiyoyin gwamnati, har ma wasu na kokarin kutsawa a cikin ginin na fadar shugaban kasa.

Kafaifan watsa labarai a kasar ta Ukraine sun ce sakamakon yanda taron gangami ya rikide zuwa tarzoma, hakan ya sa dole jami’an tsaro suka yi amfani da karfi domin tarwatsa mutane, kuma kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandar kasar Olga Bilyk ya ce, jami’ansu fiye da 100 ne suka sami raunuka.

Shi kuwa jagoran ‘yan adawa a kasar Vital Klits-choko, sake jaddawa ya yi cewar ya zama wajibi ga shugaban kasar Viktor Yanukovych ya yi murabus tare da kiran sabon zabe a cikin gaggawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.